Lionel Messi ya fashe da kuka yayin bankwana da Barcelona

 Getty Images

Dan wasan mai shekra 34 ya kwashe shekara 21 yana taka leda a Barcelona tare da samun nasarori mai yawa a wadannan shekaru.

Ya buga wasa 778 tare da jefa kwallo 627 a raga, inda ya lashe kofin La Liga 10 da kofin zakarun nahiyar Turai hudu sai kofin zakarun duniya uku, duka dai ya lashe kofina 35 a zamansa.

Tun kafin É—an wasan ya fara magana ya fashe da kuka lokacin da yake hawa dandamalin mahalarta taron suka fara masa tafi.

Messi ya fara da cewa "Gaskiya ban san da mai zan fara ba, ban kuma san me zan ce ba. Duk kwana kin nan babu abin da nake sai tunanin mai zan faÉ—a a wannan rana.

"Yanayi ne na tashin hankali bayan kwashe shekaru masu yawa anan, kusan duka rayuwata kenan. Ban shirya tunkarar hakan ba.

"A bara da ake ta rikicin tafiya ta na shirya abin da zan faÉ—a amma a yau kwata-kwata ba ni da abin faÉ—a. Ni da iyali na mun gama sakin jiki cewa muna gida," in ji Messi.


Post a Comment

0 Comments