SAƁO: Gwamnatin Kano maka Abduljabbar Kabara a Kotu

  

Gwamnatin Kano ta maka shehin malamin addinin musulunci, Abduljabbar Nasiru Kabara a babban kotun shari’a dake Ƙofar Kudu, jihar Kano.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Muhammad Garba ya sanar da haka ranar Juma’a da yamma ya na mai yin karin bayani kamar haka

” An kama Abduljabbar ne bayan samun rahoton aikata sabo, ganganci da katoɓara da ya yayi wanda ofishin Antoni Janar ya aika wa jami’an tsaro sannan da tafka saɓo kan Manzon Allah, Annabi Muhammadu SAW.

Alkalin kotun ya ɗaga shari’ar zuwa 28 ga Yuli. Sai dai kuma zai ci gaba da zama tsare wajen ƴan sanda har zuwa ranar Litinin 19 ga Yuli. Daga nan kuma sai a kai shi firzin ya ci gaba da zama har zuwa ranar da za a dawo kotu domin ci gaba da sharia.

Idan ba a manta ba tun bayan muƙabalar da aka yi tsakanin shehin malamin da gamayyar malamai a Kano, wanda Abduljabbar bai iya amsa tambaya koda ɗaya ce da aka yi masa ba, ya fito ya rika cewa ba a yi masa adalci ba.

Wannan muƙabala an yi shine kai tsaya kowa yana ji sannan ana gani.

Bayan haka ya tabbata cewa Abduljabbar dai ruwa ne ya ƙare wa ɗan kada, amma ba shi da gaskiya sannan ya aikata kantamemen saɓo.

Ya nemi a yafe masa bayan an kammala muƙabalar, sai da kuma bayan ya koma gida sai ya koma ruwa tsindim ya sake fara sakin wasu bidiyoyi na sa ya na sukar malamai da muƙabalar da aka yi.

Post a Comment

0 Comments