Rukunin farko na alhazan bana sun kammala ɗawafin farko wato Ɗawaf Al-ƙudum (ko kuma ɗawafin ƙarasowa) cikin sauƙi da nasara, a cewar kamfanin labaran Saudiyya Saudi Press Agency (SPA).
SPA ya ruwaito Shugaban Ma'aikatar Kula da Masallatan Harami, Hani Haidar, na cewa ma'aikatarsa ta samar da layuka a filin ɗawafin, wanda ke bai wa mahajjata damar yinsa cikin sauƙi.
Ma'aikata aƙalla 60 ne suka dinga kula da zirga-zirgar alhazan tare da tabbatar da cewa sun bai wa juna tazara saboda cutar korona.
Ya ƙara da cewa bisa taimakon da gwamnatin Saudiyya ke bayarwa, "za mu ci gaba da samar da kyakkyawan tsari mai nagarta don bai wa alhazai damar yin ibada cikin natsuwa".
Gwamnatin Saudiyya ta ce mutum 60,000 ne kacal kuma mazauna ƙasar za su yi aikin Hajjin na bana sakamakon annobar korona da duniya ke fama da ita.
Wannan ne karo na biyu a jere da Saudiyya hana alhazai daga wajen ƙasar gudanar da aikin saboda annobar.
0 Comments