Real Madrid Za Ta Buga Wasa Da AC Milan



Bayan da kungiyar Real Madrid ta fara atisayen tunkarar kakar wasa ta 2021 zuwa 2021 kungiyar  ta kuma sanar da za ta buga wasan sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta AC Milan.

Tsakanin kungiyoyin biyu sun lashe kofin zakarun Turai 20, inda Real Madrid ce kan gaba da 13, ita kuwa AC Milan tana da bakwai a tarhi sannan Real Madrid din za ta kara da AC Milan ranar 8 ga watan Agusta a filin wasa na Worthersee da ke Klagenfurt a kasar Austria.

Tuni kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta fara atisayen da tsirarun ‘yan wasa, bayan da wasu ke hutu sakamakon buga Copa America da Euro 2020 da wadanda za su halarci Olympic.

Real Madrid ta fara yin wasan sada zumunta domin tunkakar kakar bana da doke Fuenlabrada da ci 3-1 a Baldebebas haka kuma kungiyar za ta ziyarci Scotland, domin buga wani wasan sada zumunta a filin wasa na Ibrod da Rangers, wadda Steben Gerrard ke jan ragama.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta fara buga gasar La Liga cikin watan Agustan wannan shekarar ta 2021, inda za ta fara da ziyartar kungiyar kwallon kafa ta Alabes wadda ta dade tana buga wasannin La liga.

Sai dai wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar har yanzu basu koma fili ba sakamakon buga wasannin nahiyar turai da kuma gasar cin kofin Copa America da ‘yan wasan sukayi amma ana ganin a karshen wannan watan zasu koma.

Post a Comment

0 Comments