Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa jimillar ‘yan Najeriya 542, 576 ne su ka kammala matakin farko na yin rajistar katin zaɓe (CVR) a yanar gizo da ake gudanarwa yanzu ya zuwa ƙarfe 7 na safiyar ranar Litinin, 12 ga Yuli, wato mako biyu cif daga lokacin da aka fara aikin.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da ya yi taro a Abuja da Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe (RECs).
Yakubu ya ce hukumar ta na farin ciki da nasarar da ake samu a matakin farko na yin rajista a yanar gizo a dukkan faɗin ƙasar nan, wanda aka fara a ranar Litinin, 28 ga Yuni.
Ya ce, “Da farko, mun riƙa ba ‘yan Nijeriya bayani kan yadda aikin ke wakana a kowace rana. Kuma mun yi alƙawarin bada cikakkun bayanai na mako-mako, wanda mu ka fara a ranar Litinin ta makon jiya.
“Ya zuwa ƙarfe 7 na safiyar jiya Litinin, wato mako biyu cif tun da aka fara aikin, an samu jimillar ‘yan Nijeriya 542,576 da su ka kammala matakin farko na yin rajista a yanar gizo.
“Daga cikin waɗannan ɗin, mutum 456,909 sababbin masu rajista ne yayin da mutum 85,667 sun nemi a yi masu sauyin wurin yin zaɓe ne ko sauya katin zaɓe ko ɗora ƙarin bayani kan katin su.
“Haka kuma hukumar ta yi ƙoƙarin sama wa ‘yan Nijeriya bayanai kan yadda ake karkasa masu zaɓe a duk jihohin ƙasar nan ta fuskar shekarar haihuwa, sana’a, jinsi da kuma naƙasa.
“Daga cikin mutum 542,576 waɗanda su ka yi rajista a yanar gizo zuwa yanzu, mutum 356,777 (wato kashi 66 cikin ɗari) matasa ne ‘yan tsakanin shekaru 18 zuwa 34. Masu bi masu su ne mutum 134,719 ‘yan tsaka-tsakin shekaru waɗanda su ka kasance ‘yan shekaru daga 35 zuwa 49.
“Kashi na uku su ne masu nisan shekaru, wato ‘yan 50 zuwa 69 waɗanda a cikin su mutum 44,896 ne su ka yi rajista. Abin sha’awa, an samu dattawa 6,184 ‘yan shekaru 70 zuwa sama da su ka yi amfani da damar rajista a yanar gizo su ka yi rajistar su ma.
“A dangane da karkasa masu zaɓe bisa sana’a, mutum 156,446 ɗalibai ne; 38,217 masu sana’ar hannu; 24,421 manoma da masunta; 150,145 ‘yan kasuwa da masu tireda; 35,831 ma’aikatan gwamnati, sai kuma matan aure 8,334. Sauran 129,182 da su ka yi rajista kuma ba su faɗi sana’o’in su ba.
“Dangane da jinsi, mutum 321,781 maza ne, yayin da 220,795 mata ne.
“A ƙoƙarin mu na yi wa dukkan ‘yan Nijeriya aiki yadda ya kamata, hukumar ta buƙaci masu son yin rajista da su riƙa nuna irin naƙasar da su ke da ita (idan akwai). Hakan zai taimaka mana wajen kawo kayan aikin da su ka dace da su irin su na’urar Braille da za ta jagorance su wajen zaɓe da kuma madubin ƙara girman rubutu saboda masu buƙatar musamman a ranar zaɓe.
“Ya zuwa yanzu, mun samu bayanan masu rajista mutum 6,558 waɗanda su ka bayyana irin naƙasar da su ke da ita.”
Yakubu ya ce bayanan da ake da su na jihohi da karkasuwar sana’o’i an zuba su a gidan yanar hukumar da filayen ta na soshiyal midiya.
Haka kuma ya bayyana cewa hukumar ta amince da cibiyoyin yin rajistar ganin ido da ido guda 811, daga ranar 19 ga Yuli, domin hukumar na sane da cewa ba ko wane ɗan Nijeriya ba ne ya ke da komfuta ko babbar waya ko kuma damar shiga intanet da har zai yi rajista ta hanyar yanar gizo.
“Burin mu shi ne mu farfaɗo da cibiyoyi 2,673 inda za mu tura ma’aikata 5,346 domin yi wa mutane rajista ido da ido.
“To amma kuma bayan mun tattauna da masu ruwa da tsaki, hukumar ta yanke shawarar za ta ci gaba da aiki daki-daki ne yayin da mu ke nazarin yanayin tsaro a faɗin ƙasar nan.
“Mu da masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin tsaro, mun amince cewa mu fara daga ofisoshin mu na jihohi da na ƙananan hukumomi.
“Wannan na nufin za a fara da wurare 811 a faɗin ƙasar nan, wanda ya ƙunshi ofisoshin da ke jihohi 37 da yankin Abuja da kuma yankunan ƙananan hukumomi guda 774.
“Mun tanadar da na’urori tare da tura su faɗin ƙasar nan don ci gaba da koyar da jami’ai don shirin fara yin rajistar ido da ido.”
Ya ƙara da cewa jerin sunayen cibiyoyin guda 811, haɗi da inda su ke da kuma layukan tarho da aka tanadar wa kowane ofishin jiha ko ƙaramar hukuma a faɗin ƙasar nan, duk an wallafa su a gidan yanar INEC da shafukan ta na soshiyal midiya saboda ko wani zai yi tambaya.
“Hukumar ta na sane da cewa mun shirya fara aikin rajistar ido da ido a ranar Litinin, 19 ga Yuli. Sai dai akwai alamu da ke nuna cewa wannan rana ko mai bi mata za su kasance ranakun hutun ma’aikata.
“Haka kuma mu na sane da cewa wasu da su ka yi rajista ta yanar gizo sun sanya ranar kammala rajistar su a waɗannan ranaku da za su iya zama na hutun ma’aikata.
“Hukumar za ta yi taro a ranar Alhamis ta wannan makon domin yin nazari kan lamarin saboda a samu matsaya a kan shi.”
Ya ce jadawalin lokutan na tsawon zango huɗu na shekara ne, kuma a zangon farko za a yi rajistar masu zaɓe daga ranar 28 ga Yuni zuwa 1 ga Satumba, yayin da za a kafe sunayen masu rajistar daga 4 ga Satumba zuwa 30 ga Satumba.
Zango na biyu, inji shi, zai fara daga 4 ga Oktoba ya ƙare 20 ga Disamba inda a za a yi rajistar masu zaɓe, yayin da za a kafe sunayen masu rajista daga 24 ga Disamba zuwa 30 ga Disamba.
Ya ƙara da cewa a zango na uku za a yi rajistar masu zaɓe ne daga 3 ga Janairu 3, 2022 zuwa 22 ga Maris, 2022; yayin da za a kafe sunayen masu rajistar saboda ƙorafi ko koke, wanda za a yi daga 26 ga Maris, 2022 zuwa 1 ga Afrilu, 2022.
“Mu na aiki tuƙuru don tabbatar da cewa kamar yadda mu ka fara aikin matakin farko na rajista ta hanyar yanar gizo sumul ƙalau, shi ma fara aikin rajista na ido da ido za a yi shi ba tare da wata matsala ba.”
0 Comments