NIS Ta Ƙaryata Batun Cewa Tana Ɗaukar Aiki A Yanzu

 Ta Ja Hankalin 'Yan Nijeriya Su Yi Kaffa-kaffa Da 'Yan Damfara


Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta yi kira ga ‘Yan Nijeriya su yi watsi da batun cewa tana ɗaukar aiki a halin yanzu, inda ta ƙara da cewa ‘yan damfara ne kawai suka kitsa lamarin amma ba da yawunta ba.


Shugaban hukumar, CGI Muhammad Babandede ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ta zo ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACI Amos Okpu.


Sanarwar ta ce akwai wasu bayanai da ake yaɗawa ta kafafen sadarwa na intanet da sunan wai hukumar tana ɗaukar aiki, don haka masu buƙata su nema ta hanyar shiga wani adireshin intanet kamar haka:

 http://immigrationrecruitment.org/?p=apply-online.


Shugaban hukumar ya jaddada cewa baya ga kasancewar wannan adireshin na bogi, kwata-kwata batun ɗaukar aikin zuƙi ta malli ne. “Haka nan bayanin da suka yi na cewa wai an keɓe ranar 19 ga Yulin 2021 domin tantance waɗanda za a ɗauka aikin yaudara ce kawai da aka kitsa domin damfarar mutanen kirki masu neman aiki na halaliyarsu.”


Shugaban na NIS, Babandede yana amfani da wannan kafa wajen shawartar ‘Yan Nijeriya su yi fatali da batun da wasu ke yaɗawa na ɗaukar aikin na bogi, kana ya nanata cewa hukumar ba ta ɗaukar kowane aiki a halin yanzu.

Post a Comment

0 Comments