Messi Ya Amince Zai Ci Gaba Da Zama A Barcelona


Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi ya amince zai ci gaba da zama a kungiyar zuwa karshen kakar wasa ta shekarar 2026, sannan zai kuma karbi rabin albashin da kungiyar take biyansa.

Messi, mai shekara 34 a duniya, wanda rahotanni ke cewar yana karbar albashin fam miliyan 123, yarjejeniyarsa ta kare a Barcelona ranar 30 ga watan Yuni duk da cewa da farko anyi zaton cewa ba zai ci gaba da bugawa kaungiyar wasa ba.

Kawo yanzu dai kyaftin din kungiyar na hutu, bayan da Argentina ta lashe Copa America, kuma ba a fayyace kunshin yarjejeniyarba sai dai sake ci gaba da buga wasa da Messi zai yi yana daga cikin alkawarin da sabon shugaban Barcelona Joan Laporta ya yiwa magoya bayan kungiyar a lokacin da yake neman su sake zabensa.

A baya dai an yi ta alakanta dan wasa Messi da cewar zai koma kungiyoyin Paris St-Germain ta kasar Farana  ko kuma kungiyar Manchester City ta Ingila da ake cewar zai gaba da wasa tare da Pep Guardiola.

Har ila yau, an kuma ta cewar kyaftin din na Barcelona, wanda ya lashe kofuna da dama a kungiyar  zai koma buga gasar kwallon kafar kasar Amurka kamar yadda wasu daga cikin ‘yan wasa sukeyi idan suka fara girma.

Messi shi ne kan gaba a ci wa Barcelona kwallaye saboda kawo yanzu yana da kwallaye 672 a raga, wanda ya lashe La Liga 10 da Champions League hudu haka kuma ya ci gasar Copa del Reys guda bakwai da lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Fifa na duniya karo shida jumulla.

Wane Dan Wasa Barcelona Take Nema?

Kawo yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na kokarin yin musaya da dan wasanta, Antoine Griezmann, ita kuma ta karbi dan wasan Atletico Madrid, Saul Niguez, da nufin rage albashin da yake karba.

Tun kafin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da wannan labarin jaridun Banguardia da kuma ESPN suka bayar da rahoton cewar Messi na daf da sa hannun kan yarjejeniyar da rage albashi.

Tun lokacin da Joan Laporta ya karbi shugabancin Barcelona, yana ta kokarin rage albashin ‘yan wasa da rarrashin Messi da kashe kudi kan ka’ida kamar yadda hukumar La Liga ta gindaya.

A satin daya gabata shugaban hukumar kula da gasar La Liga, Jabier Tebas yake cewa ba za su yi wa kungiyar Barcelona sassauci ba, wadda bashin da ke kanta ya kai Yuro biliyan daya kawo yanzu.

A shekarar 2017, Messi ya saka hannu kan ci gaba da buga wasa a kungiyar Barcelona kuma mafi tsoka a duniya, in ji wani rahoto da jaridar El Mundo ta wallafa a watan Janairun wannan shekarar.

Barcelona na son gina kungiyar da fitattun ‘yan wasa domin tunkarar kakar da za a fara ta shekarar 2021 zuwa 2022, inda ta sayar da wasu daga cikin ‘yan wasanta kamar Junior Firpo da Jean-Clair Todibo da kuma Carles Alena.

Kuma hakan ne ya bai wa kungiyar damar daukar tsohon dan wasan Manchester City, Sergio Aguero da dan wasa Memphis Depay da kuma Eric Garcia, matashin dan wasa wanda shima ya koma kungiyar a kyauta.

A karshen makon daya gabata ne dan wasa Messi mai shekara 34, ya lashe kofi a karon farko a babbar tawagar Argentina, wadda ta ci Copa America, bayan doke Brazil mai masaukin baki.

A dai gasar, Messi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya taka rawar gani a Copa America tare da Neymar, kuma shine kan gaba a cin kwallaye saboda yana da kwallaye hudu a raga, kuma shi ne wanda ya fi bayar wa a zura kwallo  a raga a gasar.

Post a Comment

0 Comments