Kotu Ta Tura Sheikh Abduljabbar Gidan Yari

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

 A ranar Juma’a 16 ga watan Yuli aka gurfanar da Abduljabbar a gaban wata babbar kotun Shari’a da ke Kofar Kudu wacce ke karkashin jagoranci Alkali Ibrahim Sarki Yola.

Wata kotu a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta sa a tsare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yari.

Kafofin yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba yana cewa an gurfanar da Sheikh Abduljabbar a gaban kotu bisa tuhumar shi da ake yi da aikata sabo.

“A ranar Juma’a 16 ga watan Yuli aka gurfanar da Abduljabbar a gaban wata babbar kotun Shari’a da ke Kofar Kudu wacce ke karkashin jagoranci Alkali Ibrahim Sarki Yola.

“Ana tuhumar shi da laifukan yin sabo da tunzura jama’a.” Wata sanarwa da Malam Garba ya fitar ta ce kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.

A cewar kwamishinan yada labaran, kotun ta dage sauraren karar sai zuwa ranar 28 ga watan Yuli inda ta mika shi ga‘yan sanda don su tsare shi har zuwa ranar Litinin a tura shi gidan yari inda zai jira zuwa ranar da za ci gaba da sauraren karar.

Malam Garba ya ce, daukan matakin gurfanar da malamin a gaban kotu, ya biyo bayan fitowar rahoton farko na ‘yan sanda, wanda aka mika shi ga ofishin babban mai shari’a a jihar da kuma ofishin kwamishinan shari’a, wadanda suka shirya tuhumar Abduljabbar.

A makon da ya gabata Abduljabbar ya yi mukabala da malaman Kano inda daga baya ya fito ya ba da hakuri kan fatawarsa wacce ya yi ikirarin ba a fahimta ba.

Post a Comment

0 Comments