FFS Ta Tallafa Wa Yobe Da Motar Kashe Gobara Ta Zamani


Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yaba wa hukumar kashe gobara ta kasa (Fedwral Fire Serbice) bisa ga tallafa wa jihar da sabuwar motar kashe gobara ta zamani, tare da bayyana cewa yunkurin zai taimaka wajen daukar matakin gaggawa ta fuskar rage hadarin gobara a jihar.

Gwamnan wanda mataimakin sa, Alhaji Idi Barde Gubana ya wakilta, ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da makulan motar kashe gobarar, wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar Yobe da ke Damaturu ranar Alhamis. Yayin da kuma ya kara da cewa, wannan kari ne bisa kokarin da jihar ke yi a fannin wajen dakile asarar da tashin gobara ke haifar wa a jihar.

Bugu da kari, gwamnatin jihar ta kara da cewa ta na da kudurin tona riyoyjin burtsatse a cibiyoyin jami’an kashe gobara a fadin jihar.

Har wala yau Buni ya kara da cewa “Gwamnatin jihar ta sayo motocin kashe gobara 27, motar daukar majinyata daya tare da kayan aikin kashe gobara, kana da sake gyara shalkwatar hukumar kashe gobara a jihar da ke Damaturu.”

Haka kuma, Gwamna Buni ya bukaci samu cikalken hadin kai tsakanin hukumar kashe gobara ta kasa da jihar wajen bai wa jami’an kashe gobara a jihar karin horon sanin makamar aiki.

“Wanda ko shakka babu irin wannan hadin gwiwa zai taimaka wajen horas da jami’an kashe gobara a wannan jihar sabbin hanyoyi da matakai na zamani a ayyukan su.”

A nashi bangaren, Konturola Janar na hukumar kashe gobara ta kasa, Ibrahim Liman ya ce tallafa wa jihar da kayan kashe gobara na zamani ya zama dole sakamakon matsalar tsaron da jihar ta sha fama dashi.

Ya ce, “Haka kuma tallafa wa jihar Yobe da wannan motar kashe gobara ya zo ne sakamakon bukatar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya mika ga hukumar tare da samar da ingantattun na’urorin kashe gobara na zamani a jihar Yobe.

Post a Comment

0 Comments