Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 30 a Najeriya

Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 30 a Najeriya

A wata dayan da ya gabata mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Jigawa da ke Najeriya.

A wata dayan da ya gabata mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Jigawa da ke Najeriya.

Babban Sakataren Ma'aikatar Lafiya ta jihar Jigawa Salisu Mu'azu ya sanar da cewa, a wata dayan da ya gabata mutane sama da dubu 2 a yankunan jihar 27 ne suka kamu da cutar kwalara inda 30 daga ciki suka rasa rayukansu.

Mu'azu ya kara da cewa, tsafta na daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta a saboda haka ya bukaci jama'a da su kula tsafta yadda ya kamata.

Daga watan Janairu zuwa yanzu kuma adadin wadanda cutar kwalara ta kashe a Najeriya ya kai mutane 335.

Post a Comment

0 Comments