An kama wani Saurayi da ya yi wa kaza fyade tare da kashe ta

'Yan sanda a yankin Hafizabad da ke jihar Punjab a kasar Indiya sun kama wani saurayi mai shekaru kasa da 20 da laifin yi wa kaza fyade tare da kashe ta.

'Yan sanda a yankin Hafizabad da ke jihar Punjab a kasar Indiya sun kama wani saurayi mai shekaru kasa da 20 da laifin yi wa kaza fyade tare da kashe ta.

'Yan sanda yankin sun sanar da 'yan jarida cewa,saurayin mai shekaru 14 ya yi fyade ga kazar ne a kauyensu da ke kusa da Jalalpur Bhattian a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Mai kazar ne ya kai kara zuwa gurin 'yan sanda inda ya ce, saurayin ya dauki kazar tare da kai ta gidansu inda ya kuma yi kokarin haike mata tare da kashe ta.

Ya bayar da sunayen wasu mutane 2 a matsayin shaida.

'Yan sanda sun ce, an kama saurayin bayan an gudanar da gwaji kan kazar a asibiti. Kuma ya yi ikirarin aikata laifin da kansa. A ranar Talatar nan za a kai shi gaban kotu.

Post a Comment

0 Comments