Yaune ake fara gudanar da ibadar aikin Hajjin bana, ta shekarar 2021 da za a kwashe kwanaki biyar ana yi.
A karo na biyu a jere, Saudiyya ta rage yawan alhazan da aka ba wa izinin shiga, inda musulman da ke zaune a ƙasar dubu 60 ne kawai suka cancanci yin ibadar.
Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Saudiyya ta ce daruruwan ma'aikatan lafiya da motocin daukar marasa lafiya za su halarci taron ibadar.
Hukumomi a Saudiyya sun ce jumillar mutum 60,000 ne kacal aka yarda su gudanar da aikin Hajji na bana, a cewar shafin Haramain Sharifain mai bayar da bayanai daga masallatan Harami biyu.
Kazalika, mazauna Saudiyya ne kaɗai za su gudanar da aikin na shekarar Hijira ta 1442, waɗanda suka ƙunshi 'yan ƙasa da kuma baƙi.
Shafin ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon yaɗuwar sababbin nau'uin cutar ta korona a ƙasashen duniya.
Haka nan, rukunin mahajjata guda uku ne kaÉ—ai za a bai wa damar yin ibadar. Su ne:
- Wanda aka yi wa rigakafin korona
- Wanda aka yi wa rigakafi guda É—aya kuma ya shafe kwana 14
- Wanda aka aka yi wa rigakafi amma bai gama warkewa ba
0 Comments